bdullahi Umar Ganduje, a ranar Talata, 23 ga watan Afrilu, ya ce gwamnatin jihar Kano ce ke da hannu a dakatarwar da aka yi masa daga jam’iyyar APC.

 

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya kuma ce babu wani abin da zai ɗauke masa hankali wajen ganin ya mayar da jam’iyyar APC zaɓin talakawan Najeriya.

 

Ya yi nuni da cewa ko kaɗan bai damu da dakatarwar da aka yi masa ba wacce ya zargi gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf da kitsawa.

 

Jaridar The Pumch ta ce Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa a Abuja lokacin da ƙungiyar shugabannin jam’iyyar APC na jihohi suka kai masa ziyarar nuna goyon baya.

 

A halin da ake ciki, shugaban riƙo na ƙungiyar, Cornelius Ojelabi, ya ce sun je sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa ne domin tabbatar da goyon bayansu ga tsohon gwamnan na jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: