Wani ɗan kasuwa a Kano Alhaji Ismaila Abdullahi Yusuf ya yi kira ga matasa da su kasance masu juriya da biyayya domin samun nasara a rayuwa.

 

 

 

Alhaji Ismaila wanda shi ne shugaban kamfanonin mai na Yarima Oil da Alrayyan, ya ce matasa za su samu nasara idan su ka yi biyayya ga na gaba da su da kuma riko da gaskiya da amana

 

 

 

A tattanawar da aka yi da shi a gidan talabiji na Matashiya TV ta cikin shirin Tsaya Da Ƙafarka, ya ce mafi yawan abinda ke dakushe matasa shi ne wasu na yin son rai a lokacin da su je karkashin iyayen gidansu

 

 

 

Ya ce idan matasa su ka yi haƙuri su ka yi biyayya tare da riƙo da gaskiya da amana, babu shakka za su zama wasu a nan gaba musamman a bangaren kasuwaci.

 

 

 

Sannan ya shawarci matasa da su yi riƙo da sana’o’in hannu da kasuwanci, tare da yin haƙuri har lokacin da Allah ya tsarawa mutum arzikinsa.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: