Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu akan dokar tilasta gwaji kafin yin aure a fadin Jihar.

Mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan a shafinsa na facebook a yau Talata.

Sanarwar ta ce gwamnan ya sanya hannu akan dokar ne domin hakan ya bayar da damar tilasta yin gwaje-gwaje kafin aure domin rage haihuwar yara dauke da cutuka.

Daga cikin gwaje-gwajen da za a yi kafin aure sun hada da na cutar HIV, ciwon hanta, da kuma gwajin jini, domin tantance wadanda ke dauke da cutar sikila.

Sanarwar ta kara da cewa dukkan wanda ya bijirewa dokar tare da daura aure ba tare da wata shaida daga jami’an lafiya ba za a ci tararsa naira dubu 500 ko kuma daurin shekaru biyar a gidan gyaran hali.

Gwamnan ya sanya hannu akan dokar ne a ranar Litinin kuma za ta fara aiki ne daga ranar 13 ga watan Mayun da muke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: