Jami’an sojin Najeriya da ke aikin dakile ‘yan ta’adda a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma sun hallaka wani dan ta’adda daya tare da kubtar da mutane da dama a yankunan a ranar Talata.

 

Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a yau Laraba.

 

A wani sintiri da jami’an suke gudanarwa sun dakile wani yunkurin ‘yan ta’addan na yin garkuwa da mutane tare da kubtar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

 

Sanarwar ta bayyana cewa jami’an sun hallaka wani dan ta’addan ISWAP daya a Kauyen Kulukawiya da ke cikin karamar hukumar Nganzai ta Jihar Borno, tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda daya da kuma kubtar da wani yaro.

 

Sannan Jami’anm sun kuma samu nasarar ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna a Kauyen Agunu Dutse a karamar hukumar Kachia ta Jihar.

 

A dai Jihar ta Kaduna jami’an hadin gwiwa da jami’an sa-kai sun sake tarwatsa wasu ‘yan ta’adda a Kauyen Amale a karamar hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar, inda suka kwato bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, bindiga kirar gida guda daya da kuma adda guda daya.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: