Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa EFCC ta gurfanar da wasu mutane biyar a gaban kotun bayan ta zargesu da damfara a yanar gizo.

Hukumar reshen birnin tarayya Abuja ce ta gurfanar da mutanen biyar a gaban babbar kotun Abuja karkashin mai shari’a C.O Agashieze.
Guda cikin waɗanda aka gurfanar a kotun an sameshi da basaja a marsayin wata fitacciya tare da damfarar kuɗi dala 200.

Bayan karantawa waɗanda ake zargi lifinsu kotun ta yankewa biyu daga cikinsu hukuncin zaman gidan gyaran hali na watanni shida da watanni huɗu kowanne su ba tare da zabin biyan tara ba.

Sannan an yankewa wani Raphael hukuncin sharar ofishin yan sanda tsawon awanni biyu kullum tsawon watannishida, yayin da aka yankewa Gabriel da Owoicho hukuncin biyan tarar 50,000 kowannensu tare da sharar ofishin yan sanda tsawon kwana 30.