Gwamnatin tarayyar Najeriya ta mince da biyan tallafin wutar lantarki kaso 50 a asibitocin gwamnatin ƙasar.

 

Karamin ministan lafiya Tunji Alausa ne ya shaida haka yau Alhamis a Kaduna.

 

Ministan wanda ya je kaddamar da ayyuka a asitin tarayya na jihar, wanda aka samar da wuta mi amfani da hasken rana a bangaren wankin koda.

 

Ministan ya ce biyan tallafin lantarkin zai amfani marasa lafiyan da masu jinya.

 

Ya ce za su sauya sunan asibitocin tarayya zuwa asibitoci na musamman don baiwa kowa damar zuwa a duba shi.

 

Sannan ya roki ma’aikatan da su kwantar da hankalinsu, dangane da sace wasu likitoci wanda ya c za a kubutar da su ba da jimawa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: