Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da rahoton da ake yaɗawa cewar ta umarci kamfanin mai na ƙasa NNPC ya fara siyar da mai kan naira 1,000 kowacce lita.

Rahoton da ake yaɗawa an ce ƙaramin ministan mai Heineken Lakpobiri ne ya umarci kamfanin ya far siyar da man a kn naira 1,000 kowacce lita.

Yayin da yake mayar da martani a yau, ƙaramin ministan y musanta rahoton da ake yaɗawa.

Ministan wanda hadimarsa Nnemaka Okafor ta fitar da sanarwar a madadinsa, ta ce an yi hakan ne domin haifar da rudani.

Ta ce babu wani lokaci da gwamnatin tarayya ta taɓa baiwa kamfanin mai na NNPC umarnin ƙara farashin mai.

A don haka ba za su basu umarni ba idan za su yi za su yi ne a karan kansu.

Ministan ya ƙalubalanci kowa kan a gabatar da wata hujja ta rubutu ko hoto ko bidiyo dake nuna umarnin da ake yaɗawa.

A cewar sanarwar, ministan bai taɓa shiga hurumin kamfanin ba kuma ba zai shiga ba musamman a hukuncin da kamfanin ke ya yankewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: