Kamfanin Dangote ya gabatar da samfurin man fetur da y fara tacewa a Najeriya.

Shugaban kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangite ne ya shaida haka yau a matatar manda ke Ibeju-Lekki a jihar Legas
A jawabisa, Dangote ya ce man fetur din da matatarsa za ta fara fitarwa zai wadata Najeriya dawasu ƙasashen ketare.

Haka kuma za su fitar da kididdigar man da ake amfani da shi a ƙasar.

Shugaban kamfanin ya jinjinawa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kan jajircewarsa tare da umarnin da ya bayar don siyarwa da matatar man danyen mai kuɗin naira.
Dangote ya jinjinawa ƴan Najeriya bisa kwarin giwwa da goyon baya da ya samu.
Sannan ya ce matatar za ta hidimtawa Najeriya wajen ganin an kawo karshen wahalar mai da aka dade ana fuskanta.