Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce mutane 693 ne su ka mutu samakamon cutukan mashaƙo, lassa da cutar amai da gudawa.

Hukumar ta ce lamarin ya faru tun daga farkon shearar da mu ke ciki.
Babban daraktan Hukumar DaktaJide Idris ne ya bayyana haka yau a Abuja, yayin da yake bayani dangane da barkewar cutuka a kasar.

A cewarsa, mutane 216 cutar amai da gudawa ta hallaka, yayin da cutar Lassa ta kashe mutane 168 sai kuma mutane 309 da su ka mutu sanadin cutar mashaƙo.

Zazzabin lassa dai ya tsallaka jihohi 27 sannan ya shafi kananan hukumomi 127
Akwai wasu mutane 7,773 da ake zargi sun kamu da zazzabin lassa.
Shugaban ya ce su na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an daƙile cutukan da ke ci gaba da bazuwa a ƙasar.