Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Zamfara ta tsayar da ranar da za ta shirya zaɓen shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a jihar.

Hukumar ta ayyana ranar 16 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a yi zaɓen.
Shugaban hukumar Bala Aliyu Gusau ne ya bayyana haka a yau bayan rantsar da shi.

Ya ce za a fara siyar da fom din takarar a ranar 25 ga watan Oktoba zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba.

Shugaban y ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da aikinta karkashin doka.
Haka kuma za su ci gaba da sanar da al’umma kowanne abu da su ka yi.
