Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa ana shirye-shiryen tsige shi daga mukaminsa.

Sanata Godswill ya bayyana hakan ne a zaman da majalisar ta gudanar a yau Laraba.
Akpabio ya kuma musanta cewa jami’an tsaron farin kaya na DSS sun mamaye Majalisar domin dakile shirin tsige shi da ake yi daga shugabancin majalisar.

Shugaban ya ce majalisar na ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin aminci, kuma za su mika lamarin ga kwamitin ayyuka na musamman domin gudanar da bincike akan batun, tare kuma da mika rahotan binciken cikin gaggawa ga Majalisar.

Akpabio ya bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar wadda ba ta da tushe balle makama.