Gwamnatin tarayya ta mika sakon jaje ga gwamnatin Jihar Jigawa da ‘yan uwa da iyalan wanda suka rasa rayukansu bayan fashewar wata tankar man fetur wadda ta hallaka mutane akalla 105, tare da jikkatar 70 a Jihar.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da ofishin mataimakin shugaban Kasa Kashim Shettima ta wallafa a shafinsa na Facebook a yau Laraba.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin ta nuna rashin jindadinta dangane da afkuwar lamarin.

Shettima ya mika sakon ta’aziyyar ne ga gwamntin jihar ta Jigawa da al’umar Jihar, a madadin shugaba Kasa Bola Tinubu da ke Kasar Birtaniya.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin ta kuma bukaci da a fara yin duba akan matakan da ake bi wajen sufurin man domin kaucewa sake afkuwar hakan anan gaba.
Kashim Shettima ya kuma yi addu’ar neman gabara da rahma ga wadanda suka rasa rayukansu, tare da addu’ar neman sauki ga wadanda suka jikkata.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin ta tarayya za kuma ta tallafawa mutanen da gobarar ta shafa ta dukkanin hanyoyin da su ka dace.
A jiya Talata ne dai wata mota dakon man fetur ta fadi a garin Majiya da ke karamar hukumar Taura a Jihar ta Jigawa, wanda hakan ya haifar da mutuwar mutane da dama, tare da jikkatar wasu.