Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima zai kai ziyarar aiki kasar Sweden.

Mai magana da yawun ofishin mataimakin shugaban kasar Stanley Nkwocha ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.

Sanarwar ta ce Shettima zai tafi Kasar ta Sweden ne domin ziyarar kwanaki biyu bisa wasu yarjejeniyoyi da ke tsakanin kasashen biyu.

A yayin ziyarar Shettima zai tattauna kan al’amuran da suka shafi sadarwar zamani da ilimi, harkokin noma, al’adu, Sufuri hakar ma’adinai da dai sauransu, , duk domin kawowa Najeriya ci gaba.

Sannan Shettima zai gana da masu ruwa da tsaki na ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu a Kasar ta Sweden.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: