Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawan ta tabbatar da karin mutuwar mutane 11 daga 94 da suka rasa rayukansu a Jihar Jigawa bayan fashewar wata tamkar man Fetur a Jihar a daren Jihar Talata.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Lawal Shisu Adam ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya fitar a yau Laraba.

Shisu ya ce a halin yanzu mutane 70 da suka jikkata su na kwance a Asibiti domin ba su kulawa, yayin da kuma wadanda suka rasu aka yi jana’izarsu.

A jiya Talata ne dai wata motar dakon man fetur ta fadi a garin Majiya da ke karamar hukumar Taura a Jihar ta Jigawa, wanda hakan ya haifar da mutuwar mutane da dama, tare da jikkatar wasu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: