Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun kai hari ƙauyen Dan Auta a ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.

Rahotanni sun ce yan bindigan sun kai harin ne a jiya Juma’a.


A yayin da su ka kai harin kuma sun hallaka mutane biyu sannan su ka yi garkuwa da wasu mutane 13.
Daga cikin mutanen da su ka yi garkuwa da su har da shugaban jam’iyyar APC na yankin Alhaji Imamu.
Shaidu sun ce yan bindiga sun je da yawansu haye kan babura dauke da muggan makamai.
Yayin da jami’an sa kai na jihar Katsina ke kokarin kai dauki an hallaka guda daga cikinsu.
Rahotanni sun ce da yawan mutanen garin sun ji rauni daban-daban yayin da wasu ke karɓar magani daga jami’an lafiya.
Zuwa yanzu babu wata sanarwa daga jami’an tsaro a jihar Kan harin da aka kai.