Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya NERC ta ce na’urar rarraba wutar lantarki ce ta lalace ya sa aka samu katsewar a jiya Asabar.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da hukumar ta fitar yau bayan samun katsewar lantarki a Najeriya.


Hukumar ta ce wutar ta samu matsala ne a safiyar jiya.
Sai dai an yi kokarin yin gyaran wanda a yanzu jihohi 33 da Abuja su ka samu wutar.
Hukumar ta ce a safiyar Asabar ta samu labarin lalacewar wutar daga babbar tashar wuta ta Jebba, wanda hakan ya jefa miliyoyin al’ummar ƙasar cikin duhu.
Katsewar wutar dai ya haifar da cikas ga kamfanoni da kananan masana’antu.
Haka zalika ya haifar da ce ce ku ce ga yan Najeriya