Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a Najeriya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya c lokaci ya yi da za a duba wata mafitar maimakon wutar lantarki.

Kwanwaso ya bayyana haka ne yayin da ake tsaka da fuskantar rashin wuta a yankin arewacin Najeriya.
Fiye da mako guda kenan ake fuskantar ƙarancin wutar lantarkin wanda ya tsayar da al’amuran yankin cak.

A wata wallafa da Kwankwaso ya yi, ya ce abin takaici ne ganin yadda wasu yankunan arewacin kasar ke cikin duhu.

Kwankwaso ya ce mutane ba za su iya siyan man dizal don maye gurbin wutar lantarki ba.
A cewarsa wannan manuniya ce da ya kamata a dauki wata hanyar maimakon dogaro da wutar lantarki kaɗai.
Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya TCN ya ce an lalata hanyar rarrab wuta a jihohin Kaduna Kano, Gombe da Bauchi da wasu jihohin arewa.
Amma ya na hada kai da ofishin mashawarcin shugaban kasar kan sha’anin tsaro domin gyara matsalar.