Ƴan bindigar da suka yi garkuwa da limamin cocin katolika, a Jihar Edo Rabaran Fr. Thomas Oyode sun nemo da a ba su Naira miliyan 200 a matsayin kuɗin fansarsa.

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da limamin cocin ne a yayin da suka kai wani hari makarantarsa ta Immaculate Conception Minor Seminary da ke ƙaramar hukumar Etsako ta Gabas a Jihar a lokacin da suke gudanar da addu’o’i.

A yayin harin da suka kai makarantar shugaban makarantar da kansa ya miƙa kansa ga ƴan bindiga domin su saki ɗaliban da suka sace daga makarantar a ranar Lahadi.

Daraktan yaɗa labarai na cocin Katolika da ke Auchi, Rabaran Peter Egielewa ya tabbatarwa da manema labarai cewa masu garkuwan sun kira sun nemi kuɗin fansar kafin sakin limamin.

Wata majiya ta ce a Jihar Litinin ne maharan suka kids cocin Katolika ta Auchi, tare da bukatar Naira miliyan 200 kafin sakin limamin.

A halin yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sandan jihar ta Edo kan harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: