Wata kotun daukaka ƙara ta bayar da umarnin sake sauraron shari’ar masarautar Kano wadda aka ɗauki lokaci ana yinta.

A zaman kotun ma yau ta ce ba a yi wa sarki Muhammadu Sanusi ll adalci ba domin ba a bashi damar ji daga gareshi ba aka yanke hukuncin.
Kotun ta umarci da alƙali alkalai na Kano ya saka wani alkalin don ganin ya sake sauraron shari’ar tare da yanke hukuncin cikin gaggawa.

A cewar kotun, kotun tarayya ba ta da hurumi don sauraron ƙarar da ake yi a kan masarautar.

A zaman kotun da aka yi a yau, ta bukaci da a yi wa kowacce ɓangare adalci tare da sake umarni da a sake sauraron ƙarar tare da yanke hukuncin ba tare da bata lokaci ba.