Babbar kotun majistire da ke zamanta a Iyaganku, ta aike da wasu mutane shida zuwa gidan gyaran hali da ke birnin Badin ɗin jihar Oyo a yau Talata, bisa zargin su da aikata fashi da makami da karɓar kayan sata da kuɗin su ya kai Naira miliyan 32.

Waɗanda ake ƙarar sun haɗar da Mathew Elegbede ɗan shekaru 34, Adeleye Nurudeen mai shekaru 37, Obina David mai shekaru 39, Aromeh Friday ɗan shekaru 34, Anagaba John ɗan shekaru 35 sai kuma Chukwuka Aralia mai shekaru 56.

Za su yi jiran sauraron shari’ar ne bisa zargin aikata laifuka guda uku da suka hadar da haɗa kai da aikata laifi, fashi da makami da kuma karɓar kayan sata.

Babbar alƙaliyar kotun mai shari’a Olabisi Ogunkanmi bata karɓi koken waɗanda ake ƙarar ba, sakamakon rashin hurumin doka.

Inda ta ake da waɗanda ake zargin zuwa gidan gyaran hali na wucin gadi bisa shawarar ɓangaren gurfanar da masu laifi daga ma’aikatar shari’a ta jihar Oyo, daga bisani ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 22 ga watan Afrilun na shekarar da muke ciki.

Tun da farko dai, jami’i shigar da ƙara Copral Akeem Akinloye ya shaidawa kotun cewa, mutanen da ake ƙarar sun aikata laifin ne ranar 10 ga watan Nuwambar shekarar da ta gabata ta 2024, da misalin ƙarfe 10:30 na dare a titin Podo, da ke yankin Challenge a birnin na Badin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: