Gwamnatin jihar Borno ta yaye sabbin malamai 1,181 a karkashin shirinta na horar da malamai, don bunkasa tsarin koyo da koyarwa da ingantuwar ilimi a jihar.

Bikin yaye malaman ya wakana ne a jiya Juma’a, a kwalejin ilimi,kimiyyah da fasaha ta Umar Bin Ibrahim El-Kanemi da ke karamar hukumar Bama, a jihar ta Borno.

Da ya ke jawabi yayin taron kwamishinan ilimi, kimiyyah, fasaha da kirkira Lawan Wakilbe ya bayyana cewa, an yi tsarin ne karkashin shirin bunkasa ilimin yara mata na AGILE, wanda ma’aikatar ilimi,kimiyya da fasaha ta jihar ta assasa.

Ya kuma kara da cewa wanda dukka na karkashin yunkurin gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum na bunkasa fannin ilimi da bashi goyon baya, kamar yadda aka gani a cikin wannan shirin na horas da malamai.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: