Hedkwatar tsaro ta kasa ta bayyana cewa jami’an soji sun hallaka wasu ‘yan ta’adda 27, tare da kama 62 a wasu hare-hare da suka kaddamar kan ‘yan ta addan a cikin mako guda a sassan Kasar.

Mai magana da yawun hedkwatar Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a a Abuja ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Buba ya bayyana cewa jami’an sun kuma samu nasarar kubtar da mutane 44 da ‘yan ta’addan suka sace.
Acewar sanarwar nasarar ta samu ne tsakanin ranakun 30 ga watan Janairun da ya gabata zuwa jiya 7 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Ya ce jami’an sun kama wasu mutane 23 da ake zargi da satar man fetur, tare da kwato wasu kayayyaki da kimarsu ta kai Naira 292, 644, 100.

Har ila yau sanarwar ta ce daga cikin kayyakin da aka kwato sun hada da danyen man fetur lita 253,330, da lita 42,000 na dizal da aka tace shi ba bisa ka’ida ba, sannan lita 5,100 na man fetur.

Acewar kakakin jami’an Rundunar Operation Hadin Kai sun hallaka ƴan ta’adda 18, inda suka kama 11, da kuma kubtar da mutane 31 da aka yi garkuwa da su.

Sai Jami’an rundunar Operation Fasan Yamma sun hallaka ‘yan ta’adda takwas, tare da kama shida, da kuma kubtar da mutane 55 da aka yi garkuwa da su.

Sannan jami’an Rundunar Operation Safe Haven sun hallaka ‘yan ta’adda huɗu, sun kubtar da mutane 13 a yankin Arewa ta Tsakiya.

Har ila yau jami’an Rundunar Operation Delta Safe sun kama mutane 23 da ake zargi da satar man fetur, tare da lalata haramtattun guraren tace mai, da kwato makamai da harsasa.

Bugu da kari jami’an Rundunar Operation Whirl Stroke kuma sun hallaka wani dan bindiga daya, inda suka kama mutane 30 da ake zargi da aikata ta’addanci.

A yankin Kudu maso Gabas kuma jami’an soji sun kama ‘yan ta’addan kungiyar IPOB biyar, tare da lalata abubuwan fashewa, da kuma kubtar da mutane hudu da aka yi garkuwa da su.

A karshe jami’an sun kuma kwato makamai 61 Da harsasai 1,584.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: