Kimanin mata 200 ne su ka amfana daga horon sana’ar kiwon kifi, karkashin shirin hukumar bunkasa harkokin noma da kiwo na gwamnatin Jihar Bauchi.

Hukumar ta shirya bayar da horon ne bisa haɗin guiwa da mata ƴan kasuwa, da kuma kungiyar haɗin kan masu sana’ar noma da kiwo.

Shugaban shirin na hukumar wato Ya’u Muhammad, shi ne ya bayyana adadin yawan matan da su ka amfana daga horon a yau Asabar a jihar ta Bauchi.

Inda ya ƙara da cewa, gwamnatin Jihar ta himmatu wajen tallafawa mata da kuma bunƙasa noman na kifi, inda horon ya fi karkata ga dabaru na zahiri a sana’ar ta kiwon kifi.

Inda ya bayyana cewa wasu daga cikin muhimman abubuwan lura ga kiwon kifi sun haɗar da zaɓar inda ya dace don kiwon, da kuma gano sahihiyar hanyar samun ruwan yin kiwon kifin.

A ƙarshe ya kuma ƙarfafi samar da hanyar da ta dace, don yin kasuwanci bayan samar da kifin da dangoginsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: