Babban hafsan tsaro na Najeriya Christopher Musa ya tabbatar da kashe wasu jagororin yan ta’adda wato Kachalla Gwammade da Kachalla Shehu da yaransu hudu, dukkanninsu a jihar Zamfara.

Ya bayyana hakan ne dai yayin rufe babban taron hadakar tsaro na manyan kwamandojin rundunonin tsaron Najeriya, a babban birnin tarayya Abuja.
Inda kuma ya bayyana cewa sumamen da aka kai ya matukar dugunzuma babban jagoran yan ta’addan nan wato Bello Turji, inda ya yi ta gudun neman mafaka tare hanyar tsira da ransa.

Sumamen dai an wanzar da shi ne karkashin rundunar tsaron da shirinta mai taken ”nuna rashin tausayi”, a kauyen Ruwan Dawa da ke karamar hukumar Maru a jihar ta Zamfara.
