Rundunar ‘yan sandan Jihar Edo ta ce jami’anta sun kubtar da wani basarake da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Moses Yamu ya fitar a yau Asabar, ya ce jami’an sun kubtar da Basaraken ne a jiya Juma’a.

Kakakin ya ce jami’an sun samu nasarar ne, bisa hadin gwiwa da gwamnatin Jihar, da ‘yan Sa-kai, mafarauta da kuma mazauna yankin.

Yamu ya kara da cewa hadakar jami’an sun kubtar da basaraken, sakamakon gudanar da aiki tukuru har ta kai ga sun kubtar da shi.

Rundunar ta kuma godewa gwamnan Jihar Sanata Monday bisa gudummawar da ya bayar wajen ceto basaraken.

Leave a Reply

%d bloggers like this: