Tsohon gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana cewa, Najeriya ba za ta taɓa cimma gamsashshen ci gaban tattalin arziki ba matukar ta ci gaba da dogara akan shigo da kayayyaki zuwa ƙasar.

Masari ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da shirin ƙasa Najeriya na gano masu basira, yau Asabar a birnin tarayya Abuja.

Taron wanda haɗin guiwa ne da hukumar ilimin fasaha ta ƙasa, bisa kudirin zaƙulo matasa masu fikira a faɗin Najeriya.

Tsohon gwamnan ya ƙarfafi bukatar samar da abubuwan amfani a cikin gida, don ƙara haɓaka tattalin arzikin ƙasar.

Masari ya bayyana cewa ba za a taba samun ci gaba ta hanyar shigo da kayayyaki daga ƙasashen ƙetare ba, inda ya kafa hujja da cewa kuɗin ƙasar ba zai taba yin daraja ba.

Masarin wanda shi ne shugaban kwamitin asusun tallafawa manyan makarantu na TETFUND ya ƙara da cewa, akwai alfanu ƙwarai da gaske a tallafawa marasa ta hanyar horar da su sana’o’in dogaro da kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: