Ministan ayyuka na Najeriya David Umahi ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta na duba yiwuwar sanya shingayen karɓar haraji a wasu titunan Najeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin da ya ke rangadin duba yadda aikin titi mai hannu biyu daga Abuja zuwa Kaduna ya ke gudana.

Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin tarayya na yunkurin yin haɗaka da al’ummu masu zaman kansu, don bunƙasa tituna a faɗin Najeriya, da haɓaka tattalin arzikin al’umma.

Kamar yadda ya bayyana cewa, su na duba yiwuwar sanya shingayen karɓar harajin a manyan titunan da ke shiyyoyin siyasa guda shida na Najeriya, don samun damar kula da lafiyar titunan.

Sai dai ya bayyana cewa ba za su saka shingen a duk wani titi da ba a kammala aikinsa ba, dole sai an tabbatar da gama shi 100 bisa 100.

Umahi ya ƙara da cewa, titunan da aka daɗe da gama su kuma su ka lalace, za su cimma yarjejeniya da masu ruwa da tsaki don kula da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: