Sojojin ruwa a Najeriya ƙarƙashin rundunar Operation Delta Sanity 2, sun samu nasarar kama wasu mutane tara da ake zargi da aikata laifin satar ɗanyen man fetur a jihar Akwa Ibom.

Babban kwamandan rundunar NN Jubilee Commodore Abubakar Umar ne ya bayyana hakan, a wata tattaunawarsa da manema labarai jiya Asabar, a Ibaka da ke ƙaramar hukumar Mbo a jihar ta Akwai Ibom.
Ya bayyana cewa babban hafsan sojojin ruwan Vice Admiral Emmanuel Ogalla, shi ne ya ƙaddamar da rundunar ta Operation Delta Sanity 2 a watan Disambar shekarar 2023, a matsayin ci gaba da ayyukan rundunar Operation Delta Sanity 1.

Inda ya ce babban aikin rundunar tsaron shi ne kula da satar ɗanyen mai, fasa bututun man da safarar sa, fashi da makami a cikin teku, da kuma sauran laifukan da ake aikatawa a cikin ruwan.

Inda ya ƙara da cewa babbar manufarsu ita ce, kiyaye zurarewar ɗanyen mai da kuma haɓaka samar da shi da yawansa a Najeriya.
Inda ya tabbatar da kama wani kwale-kwale na katako mai ɗauke da mutane tara (9), waɗanda ake zargin su da aikata na satar ɗanyen man a cikin tekun.
