Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya koka da yawan haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar, in da ya ce hakan ya na shafar ƙin shiga makaranta.

Mutfwang ya yi wannan kalami ne dai bayan aikin ibada ƙarshen mako, a wata coci da ke birnin Jos a jihar Filato.
Sannan ya yi kira ga shugabannin addinai da kuma iyaye, da su bayar da goyon baya ga gwamnatin a ƙoƙarinta na shawo kan matsalar.

Ya kuma furta cewa haƙar ma’adanan ba bisa ka’ida ba ya bayar da gudunmawa sosai, wajen ƙara yawan mutanen da su ke daina zuwa makaranta a jihar.

Da ya ke ci gaba da bayanin illolin da matsalar ke janyowa, Caleb ya ce aikin ya fi tsamari a kananan hukumomin Bassa, Riyom, Jos Ta Kudu da kuma Barikin Ladi.
Ya ce makarantun da su ke yankunan kusan duk babu ɗalibai, saboda matasa maza da mata sun yi watsi da su sun koma aikin haƙar ma’adanai.