Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya gargaɗi gwamnatin tarayya da cewa, ikirarin cewa dabbobi kamar macizai da birrai su na haɗiye kuɗaɗen al’umma Sam ba abun lamunta ba ne.

Inda ya ce hakan bai kamata ya zamto wani abu da zai faru ba, ga kuɗaɗen da aka ware na lura da muhimmin bangaren lafiya a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025.
A wani jawabinsa na jiya Lahadi, Atiku ya bukaci gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ta dinga yin komai a bude, dangane da yadda ake ware kuɗaɗen kula da kowanne bangare.

Atiku ya kuma kara jaddada muhimmanci kyakkyawan shugabanci, da bayyana cewa ya kamata a kashe duk wani kudi yadda ya dace, don haɓaka bangaren lafiya a ƙasar.

Ya ce a shekarun nan akwai wasu zantuka marasa manufa na zargin wasu dabbobi akan ɓatan kuɗin al’umma, inda ba a taba yunkurin yin bincike ko hukunci dan kaucewa sake faruwar hakan a nan gaba ba.
A karshe ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi abinda ya dace ta hanyar bibiyar kudin da aka ware cikin kasafin kuɗi, kimanin Dala biliyan ɗaya da miliyan 700 dan kula da bangaren lafiya.