Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da hadin gwiwa da hukumomin tsaro a Jihar, don ganin an samu tabbataccen zaman lafiya a fadin Jihar.

Gwamna Bala ya bayyana haka ne a jiya Alhamis, a lokacin da Shugaban rundunar Ayyuka na Musamman na Sojin Saman Jihar AVM Eniobong Effiong ya ziyarce shi, a lokacin da ya ke shirin yin ritaya.
A wata sanarwa da hadimin gwamnan Lawal Mu’azu ya fitar, ya ce Gwamna Bala ya kuma yabawa Eniobong bisa gudunmawar da ya bayar wajen inganta tsaro a Jihar.

Gwamna ya kuma bukaci rundunar Sojin Sama ta Kasar da ta ci gaba da gudanar da sintirin da jiragen yaki a Jihar, musamman a yankunan iyakokin jihar Bauchi, domin haramta ayyukan batagari a Jihar.

Acewarsa hadin gwiwa tsakanin Sojin Sama da kuma sauran hukumomin tsaro hakan zai taimaka matuka wajen tabbatar da zaman lafiya da dakile miyagun laifuffuka a jihar.
A yayin jawabin Eniobong ya mika godiyarsa ga Gwamna Bala bisa goyon bayan da yake bai wa jami’an Sojin Sama wajen gudanar da ayyukansu a Jihar ta Bauchi.