Gwamnatin tarayya ta bayyana kudurin kafa rundunar tsaro ta musamman da za ta yi aikin tsare cibiyoyi da layukan samar da wutar lantarki Kasar, domin kawo karshen masu satar kayan wutar.

Ministan cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a yau Juma’a a yayin wata fira da Channels TV.

Olubunmi ya bayyana cewa za su taki matakin ne tare da hadin gwiwar Ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu, wajen kama rundunar mai taken ”Rundunar tsaron lantarki” a Kasar.

Har ila yau ya ce za su samar da rundunar ne daga hukumar tsaron fararen hula ta Civil Defence, tare da dora musu nauyin dakile lalata kayayyakin lantarki.

Acewarsa hakan zai taimaka matuka wajen kawo karshen katsewar layikan wuta a Kasar da kuma satar kayayyakin wutar daga masu satarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: