Sakamakon gabatowar watan azumi hukumar Hisbah ta bukaci masu aikata laifuka da su ka sabawa shari’ar musulunci da su tuba tare da komawa ga Allah.

Mataimakin babban kwamandan hukumar Sheik Mujahideen Aminudden ne ya yi kiran a yayin bayani dangane da kama katan din giya 115 a wani sumame da su ka kai a jihar.
Cikin jawabinsa a yau Juma’a , ya ce sun kama giyar ne a jiya Alhamis a unguwar Sabon Gari a jihar.

A cewarsa, wanda su ka kama a shagon sun taɓa kamashi a shekarar 2024 da ta gabata tare da gargadinsa a kan ya daina amma bai daina ba.

Bayan samun labarin cewar ba su daina ba su ka sake kai sumame tare da kama katan din giya 115.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da aikin tabbatar da kawar da dukkan wani abu da ya sabawa koyarwar addinin musulunci a jihar.