Sakamakon karin kudin kiran waya, data da aika sakonni kamfanin sadarwa na MTN ya bai wa ƴan Najeriya haƙuri bisa karin da ya aiwatar.

Kamfanin MTN ya yi karin kuɗin kira daga naira 7.8 kowanne minti zuwa naira 13.8.

Haka kuma kamfanin ya yi karin kudin aikewa da sakonni daga naira 4 zuwa naira 6.

Kamfanin ya ce ya na sane da cewar karin bai yi wa yan ƙasar daɗi ba a don haka ya na mai ba da haƙuri.

Karin da kamfanin ya yi ya kai da kaso 76.92 fiye da kaso 50 da gwamnatin tarayya ta amincewa kamfanonin su yi

Daga wani bangare na siyan data kamfanin ya yi karin da kaso kusan 200.

Kamfanin ya bukaci abokan huldarsa da su kara haƙuri a kan karin da su ka yi wanda su ka ce sun san bai yi wa yan ƙasar daɗi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: