Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ya jinjinawa hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas NEDC bisa saka hannun jari a fannin ilimi domin fitar da yankin daga kangin talauci.

Shettima na wannan yabon ne a yayin wata ganawa da shugabannin hukumar ta raya yankin Arewa Maso Gabas a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, tare da bashi rahoto kan ci gaban shirin fasahar ilmi ta zamani ASSEP.

Mataimakin shugaban ya kuma sake yabawa hukumar da Dr Masha bisa inganta shirin ASSEP.

Acewar Sheetima samar da ababan more rayuwa abu ne mai kyau, inda ya ce zuba hannun jari da hukumar ta yi da shirin na ASSEP hakan zai sauya fasalin yankin baki daya.

Har ila yau Shettima ya ce tsarin amfani da na’urar Virtual Reality da shirin ya samar, abu ne mai kyau da zai kuma canza yadda dalibai ke koyon karatu, da kuma malamai da makarantu, wanda hakan ke kara inganta fannin koyo da koyarwa.

Acewar Shettima tarihi ba zai taba manta da irin gudunmawar da hukumar ke bayarwa ba wajen farfado da yankin, inda ya bukaci Ma’aikatar Raya Yankunan Kasar nan da sauran masu ruwa da tsaki da su hada kai don samar da sakamako mai kyau a cikin ayyukan su.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: