Hukumar hana fasa kwauri a Najeriya kwastam ta mika bindigu 1,599 da kunshin harsashi 2,298 ga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaron ƙasa.

Jami’an sun kama makaman ne a jihar Legas yayin da ake kokarin shigo da su Najeriya.
Babban kwamandan hukumar na ƙasa Adewale Adeniyi ne ya mika makamn ga cibiyar kula da mannya da kananan makamai ta kasa karkashin ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribadu.

A cewar kwamandan hukumar, hukumar ta himmatu wajen tabbatar da tsaron kasar ta hanyoyin kula da iyakokinta.

Sannan za su ci gaba a kan sa ido da kula da abubuwan da ake shiga da fita da su.
Babban mai ba shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya yabawa hukumar tate d kira a gareta da su kara hada kai da sauran jami’an tsaro.
Daraktan cibiyar kula da manya da kananan makamai Janar Johnson Kokumo da ya wakilceshi ya ce gwamnatin tarayya ba za ta gajiya ba wajen hana yaduwar makamai a cikin ƙasar.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da jami’an kwastam ke kama makamai d ake kokarin shigo da su Najeriya ba.