Hukumar daƙile cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta ce zazzabin lassa ya halaka mutane 70 cikin wata guda.

Hukumar ta tabbatar da mutane 358 da sh ka kamu da cutar yayin da ake zargi ta kama mutane 1,552.

Jihohin Taraba, Ondo da Odo na kan gaba cikin waɗanda aka fi samu rahoton masu kamuwa da cutar.

Rahoton ya ce cikin jihohi goma mutum guda aka tabbatar ya kamu da cutar cikin kananan hukumomi 58 na jihohin.

Sai dai a jihar Taraba mutane 18 cutar ta halaka yayin da ta halaka mutane 17 a Ondo, sai jihar Edo da cutar ta halaka mutane 11.

A Ebonyi kuma cutar ta kashe mutane shida, sai Bauchi da cutar nan ma ta kashe mutane shida sannan Gombe da cutar ta kashe mutane biyar.

A jihar Kogi kuwa mutane huɗu cutar ta kashe sai Nassarawa da cutar ta kashemutane biyu sai Filato da cutar ta halaka mutum guda.

Rahoton ya ce kashi 75 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar sun fito ne daga jihohin Ondo, Edo, Bauchi yayin da kaso 25 su ka fito daga sauran jihohi bakwai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: