Ofishin jakadancin Kasar Canada a Najeriya ya bayyana cewa ba zai ce uffan ba akan dalilin da ya sanya aka hana hafsan tsaron Kasar nan Janar Christopher Musa da wasu jami’an sojin bizar shiga Kasar ta Canada ba.

A wata sanarwa da ofishin ya fitar a yau Juma’a Abuja, ta ce sakamakon dalilan sirri da kuma tsare-tsare ba zai ce komai ba dangane da lamarin.
Acewar sanarwar dalilin tsare sirri ne ya sanya ba za su ce komai ba akan batun hana Christopher Musa da wasu jami’an tsaron Kasar shiga Canada, bayan gayyatarsu da aka yi zuwa taron girmama tsofaffin Soji.

Bayan hana Christophe Musa shiga Kasar ta Canada hakan ya haifar da zazzafan martani a Kasar, tare da nuna rashin jindadi da yadda Kasar ta Canada ta hana Jami’an tsaron Kasar Biza.
