Hukumar zabe Mai zaman Kanta ta Kasa INEC ta Jihar Sokoto ta tabbatar da konewar ofishinta da ke cikin Ƙaramar hukumar Gwadabawa a Jihar, bayan tashin gobara a Ofishin.

Kwamishinan hukumar ta INEC a Jihar Mista Sam Olumekum ne ya tabbatar da hakan a jiya Juma’a, ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sam ya bayyana cewa rahoto na farko daga ofishinsu na jihar ya bayyana cewa an samu karuwar wutar lantarki kafin faruwar lamarin.

Acewarsa gobarar ta tashi ne a ranar 11 ga watan nan na Fabrairu, inda ta lalata dukkan kayayyakin zabe da sauran abubuwa masu amfanin hukumar.

Mista Sam ya ce daga cikin kayayyakin da suka lalace sun hada da Kujeru, Tebura, da kayan aiki da kayan zaɓe da wanda ake ɗauka, da suka hada da akwatunan zaɓe 558, rumfar kada kuri’a 186, jakunkuna 186 na zaɓe, tabarmi 400, bokitan robobi guda 300 da sauransu.