Rundunar yan sandan Najeriya ta hallaka wasu mutane hudu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi da kuma kwato Naira miliyan uku, a karamar hukumar Suru da ke jihar Kebbi.

Mai magana da yawun rundunar a jihar CSP Nafi’u Abubakar ne ya sanar da hakan, cikin wani jawabi da ya fitar a yau Asabar.
Ya ce a daren jiya Juma’a ne da misalin karfe 1;45 wasu mutane dauke da makamai da ake kyautata aton masu garkuwa da mutane ne, su ka mamaye kauyen Gobiraje da ke karamar hukumar ta Suru a jihar Kebbi, su ka dauke wani mutum mai suna Umaru Bawa dan shekaru 60.

Inda biyo bayan samun rahoton, shugaban rundunar yan sandan yankin ya tashi tawaga tare da aika su zuwa wurin da abin ya faru, inda suka tarfa yan bindigar a dajin Tundafari da ke kan mahadar Dakingari tare da yin musayar wuta da su, inda aka kashe hudu daga cikinsu, tare da kama wani biyo bayan tserewar sauran zuwa cikin jejin dauke da harbin bindigu a jikinsu.

Abubakar ya ce yan sandan sun samu nasar kubutar da wanda aka sace ba tare da komai ya same shi ba, da kuma kwato Naira miliyan uku da aka riga aka biyan yan ta’addar a matsayin kudin fansa.