Shugaban Kasa Bola Tinubu ya mika sakon ta’aziyyarsa bisa rayuwar shugaban kungiyar Yarbawa ta Afenifere Ayodele Adebanjo.

Shugaba Tinubu ya aike da sakon ta’aziyyar ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya fitar.

Tinubu ya bayyana shugaban na Afenifere a matsayin haziki kuma jajirtace, da ke kokarin tabbatar da Kasa daya da kuma dimkuradiyya.

Shugaba Tinubu ya ce Adebanjo na daya daga cikin wadanda suka jajirce wajen gina Najeriya, tare da damawa dashi a harkokin siyasa.

Shugaban ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga ‘yan uwa da iyalan marigayin da kuma kungiyar Afenifere, da gwamnonin yankin kudu maso yammacin Kasar nan bisa rashin da aka yi.

Shugaban kungiyar ta Afenifere ya rasu ne a jiya Juma’a a gidansa da ke Jihar Legas, ya kuma ya rasu ne yana da shekaru 96 a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: