Gwamnatin jihar Neja ta sanar da ƙudurinta na raba manyan motocin kayan abinci guda 1,000 akan farashi mai sauƙi a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar 25, a matsayin tallafi ga al’ummar jihar duba da gabatowar azumin watan Ramadan.

Gwamnan jihar Umar Bago ne ya sanar da wannan ci gaban, yayin ganawa da masu ruwa da tsaki a gidan gwamnatin Jihar da ke Minna.

Bago ya ƙara da cewa dalilin ganawar ta su na da alaƙa ne da yadda za a tsara saukar da farashin kayan abinci, ga al’ummar jihar a lokacin gudanar da ibadar azumin watan Ramadan.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar bisa haɗin guiwa da wani ɓangare mai zaman kansa na Niger Foods, sun girbe miliyoyin ton-ton na kayan abinci, waɗanda za su wadatar da al’ummar jihar.

Yayin da kowacce ƙaramar hukuma za ta karɓi mota goma ta kayan abinci duk bayan kwana goma a cikin watan na Ramadan, wanda za a siyar da shi a bisa sauƙaƙƙen farashi.

Gwamna Bago ya ƙara da cewa za a dinga siyar da kayan abincin mai sauƙi da kaɗan-kaɗan, dan tabbatar da kowa ya samu damar mallaka, Daɗin daɗawa kuma, za a raba motoci 500 kyauta ga al’umma marasa ƙarfi a faɗin jihar.

Ya kuma gargaɗi masu alhakin siyar da kayan abincin da su yi aiki bisa nagarta, tare da cewa duk wanda aka kama da rashin gaskiya zai fuskanci hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: