Gwamnatin Tarayya ta buƙaci bankin duniya da ya bata sabon bashin Dala miliyan 300, dan bunƙasa ɓangaren kula da harkar lafiya a Najeriya.

Sanarwar da aka samo daga bankin na duniya ta nuna cewa ana duba yiwuwar bayar da bashin, wanda za a yi amfani da hukumar daƙile yaɗuwar cututtuka ta ƙasa NCDC wajen karɓar sa a madadin gwamnatin tarayyar.
Kamar yadda bankin duniyar ya wallafa a shafinsa na yanar gizo, shirin karɓar bashin ana sa ran zai haɓaka haɗakar yankuna da kula da tsarin kiwon lafiya a kasa Najeriya.

Ana sa ran dai bankin duniyar zai amince da bayar da bashin nan da 30 ga watan Yulin 2025 bayan an gama bin diddigi, wanda aka shirya yi ranar 15 ga Afrilun 2025.

A cikin ƙunshin buƙatar bashin an gano cewa, shirin tsaron lafiya na ƙasa Najeriya ya yi daidai da ƙoƙarin gwamnati na kula da cututtuka, bayar da agajin gaggawa da kuma bunƙasa ɗakunan gwaje-gwaje a faɗin jihohin Najeriya da ma birnin tarayya Abuja.
Shirin zai ƙuduri aniyar bunƙasa haɗakar yankuna da ƙarfafa harkokin kiwon lafiya a Najeriya, kuma ya shiga cikin shirin saka hannun jarin bankin duniya a harkar lafiya, cimaka da kuma yawan al’umma a yammacin Afirka da kuma tsakiyarta.