Kamfanin samar da man fetur na ƙasa NNPCL ya musanta wani iƙirari cikin wani hoto mai motsi da ya karaɗe shafukan sada zumunta, akan rashin ingancin man da su ke samarwa.

Mai magana da yawun kamfanin Olufemi Soneye ne ya, sanar da hakan a jiya Asabar, yayin da ya ke mayar da martani game da Iƙirarin da ake cewa man da NNPCL ta ke samarwa bai kai ingancin na matatar Dangote ba.

Hoton mai motsi ya nuna inda wani mutum ke amfani da ƙananan injinan Janareta don banbance ingancin man daga ɓangarorin biyu, inda a ƙarshe ya ce man da kamfanin MRS su ke siyarwa na matatar Dangote ya fi ɗaukar lokaci wajen yin amfani fiye da na kamfanin NNPCL.

Sai dai a cikin wani jawabi kamfani NNPCL ya bayyana Iƙirarin a matsayin labarin ƙanzon kurege, tare da cewa an samo shi ne da bincike marar ma’ana da ba a tabbatar da sahihancinsa ba, wanda bashi da wata madogara ko ƙima.

NNPCL sun ce man su ingantacce ne da ake samar wa daga kyakkyawan mahaɗi, kuma yana da nagarta da ɗaukar tsawon lokaci ya na aiki da kuma kiyaye muhallin al’umma daga gurɓacewa.

Ya kuma bayyana cewa kamfanin na NNPCL zai ɗauki matakin shari’a akan duk wasu rukuni ko kuma ɗaiɗaikun mutane, da suke ƴada zarge-zarge marar gaskiya ga kamfanin na NNPCL da kuma kayayyakinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: