Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya karɓi Sanata Uba Sani tare da wasu jiga-jigan ƴan siyasa a jihar, zuwa jam’iyya mai mulkin Najeriya ta APC.

Uba Sani ya kuma tabbatarwa da Shehu Sani da sauran jiga-jigan ƴan siya guda 49 da su ka sauya sheka zuwa jam’iyyar ta APC cewa, za su ribatu da duk wata dama da ƴanci kamar sauran ƴan jam’iyyar da su ka daɗe a cikinta.

Gwamnan ya yi wannan kalami ne yayin da ya ke jawabi ga taron al’umma magoya bayan jam’iyyar, a wani gangamin taron motsa jam’iyya da ya gudana jiya Asabar a Murtala Square da ke Kaduna.

Ya kuma buƙaci dukkan waɗanda su ka sauya sheƙar zuwa jam’iyyar , da su sanar da sauran magoya bayansu cewa Ƙofar jam’iyyar ta APC a buɗe ta ke don karɓarsu zuwa cikin jam’iyyar.

Inda ya kuma ƙara da cewa babu wata jam’iyya da za ta kayar da APC a jihar Kaduna, yankin arewa da ma faɗin Najeriya baki ɗaya, a zaɓe mai zuwa kuwa ƴan Najeriya za su zaɓi jam’iyyar ne sak daga sama har ƙasa.

Cikin jiga-jigan ƴan siyasar da su ka sauya sheka zuwa jam’iyyar ta APC akwai tsohon gwamnan jihar Mukhtar Ramalan Yero, Sanata Shehu Sani, tsohon ɗan takarar gwamnan a jam’iyyar NNPP a zaɓen da ya gabata na 2023 Suleiman Hunkuyi da kuma Alhaji Sani Sha’aban wanda shi ma tsohon ɗan takarar gwamna ne.

Sauran sun haɗar da Sanata Ɗanjuma Laah, Alhaji Abubakar Mustapha tsohon sakataren tsare-tsare na jam’iyyar PDP da kuma Ambasada Sule Buba tsohon jami’in diplomasiyya wakilin Najeriya a ƙasar Koriya ta Kudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: