Hukumar shirya jarabawar kammala sikandire ta yammacin Afirka WAEC ta saki sakamakon jarabawar ɗalibai na shekarar 2024, na makarantu masu zaman kansu karo na biyu.

Adadin ɗalibai 2,577 ne dai aka riƙe sakamakon nasu, bisa zarginsu da laifin satar amsar jarabawa.

Jawabin hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Lahadi, ta hannun shugabar sashin hulɗa da jama’a a hukumar ta WAEC ta riƙon ƙwarya Moyosola Adesina.

Kamar yadda Moyosola ta sanar, adadin ɗalibai 62,023 ne suka zauna jarrabawar a faɗin Najeriya tsakanin 25 ga watan Oktoba zuwa 20 ga watan Disambar 2024, a cibiyoyin gudanar da jarabawar daba – daban na faɗin ƙasar.

Ta kuma ce adadin ɗalibai 34,878 wato kashi 53. 64 sun samu adadin credit biyar zuwa sama a darussa aƙalla guda biyar, ciki har da na yaren Turanci da kuma lissafi.

Inda ta shawarci ɗaliban da su ziyarci shafin yanar gizo na hukumar duba sakamakon nasu, kafin samun damar karɓar takardar ta su daga hukumar a hannunsu.

Ta kuma yi kira ga waɗanda aka riƙe sakamakonsu, da su ziyarci shafin yanar gizo na hukumar ta WAEC ɓangaren satar jarrabawa, dan su kare kansu akan Zarge-Zargen da ake musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: