Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya bayyana damuwarsa game da yawan kutsen malamai cikin harkokin siyasa, inda ya ce yanzu malamai su na matuƙar kwaɗayin samun iko akan masu zaɓe da kuma harkokin gudanar da siyasa.

Lamido ya yi wannan kalami ne a cikin wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, yayin ziyarar ta’aziyya ga Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun a Kaduna, biyo bayan rashin babban ɗan sa da ya yi.
Tsohon ministan harkokin wajen na Najeriya ya bayyana cewa yanzu malamai sun samu ikon sarrafa dandalin siyasa, inda su ke yin yaƙin neman zaɓe wani ɗan takara a buɗe kuma su umarci magoya bayansu da da wanda za su zaɓa.

Lamido ya ce duk da baiwar da Allah ya yi musu na zamtowa jagororin addini yanzu su na ƙoƙari ne don samun iko, sai dai kuma malaman kamata ya yi su zamo masu ɗora ƴan siyasar a hanyar da ta dace amman tunda su na son iko, to su ƴan siyasar za su koma gefe su basu fagen.

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa kamar yadda jam’iyyun siyasa su ke fama da rikicin cikin gida to su ma haka malaman addinin su ke fama da rarrabuwar kawuna, tare da gargaɗin cewa dandalin siyasar Najeriya zai ci gaba da zama cikin rikici har sai an samar da haɗin kai.
Idan za a iya tunawa dai a shekarun baya, an ga yadda shugabannin addinai su ka dinga wayar da kan mutane akan karɓar katin yin zaɓe, da kuma yayin zaɓen shekarar 2023 yadda aka samu rabuwar kai a masallatai da coci-coci wajen tallan yan takara.
A kwanan nan kuma an ga yadda batun taron makaranta Al-Qur’ani da aka shirya yi ya yamutsa hazo, inda aka yi niyyar tara mutane 30,000 ma rubuta, makaranta da mahaddatan Qur’ani.