Kimanin ƴan Najeriya 201 ne a sansanin masu ƙaura zuwa ƙasashen waje su ke dakon a kwaso su zuwa gida Najeriya daga ƙasar Amurka, sakamakon sabuwar dokar tsarin baƙin haure ta shugaban ƙasar Amurka Donald Trump.

Kuma tuni mutane 85 daga cikinsu aka gama tantance su, dan fitar da su daga ƙasar cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.

Ta bakin jakadan ƙasar ta Amurka a Najeriya Richard Mills Junior, wasu daga cikin rukunin farko na mutanen da za a dawo da su suna tsare a gidan kurkuku a ƙasar ta Amurka.

Ya kuma ƙara da cewa za a kwaso su ne zuwa birnin Legas na Najeriya, sai dai bai faɗi sahihin lokacin yin hakan ba.

Ya yi wannan jawabin ne dai yayin ganawarsa da ƙaramar ministar harkokin wajen Najeriya Bianca Odumegwu – Ojukwu a ofishinta.

Shugaban na Amurka dai na ci gaba da tabbatar da alƙawurran da ya yi lokacin yakin neman zaben, na korar baƙin haure da su ke zaune ba bisa ka’ida ba a ƙasar.

Inda tuni ya kora mutane daga ƙasar ƴan asalin ƙasar Colombia, Mexico da Indiya zuwa ƙasashensu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: