Dan takarar shugaban Kasa a Jam’iyyar Labour Party Peter Obi, ya jinjinawa Janar Badamasi Badamasi bisa namijin kokarin da yayi na farfado da tattalin arzikin Najeriya a zamanin mulkinsa.

Obi ya kuma bayyana cewa Najeriya ta kara tabarbarewa fiye da lokacin tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida bayan ya sauka daga kan mulkin Kasar a shekarar 1992.
Obi ya bayyana hakan ne ta cikin wata wallafa da yayi a lokacin da yake fadin albarkacin bakinsa bayan kaddamar da littafin tarihin rayuwar Janar Babangida mai suna ‘A Journey in Service’ a jiya Alhamis a Abuja.

Peter Obi ya ce gudunmawar da Babangida ya bayar a fannin tattalin arzikin Najeriya, da bangarorin kasuwanci da bunƙasar kamfanoni masu zaman kansu ba za a iyakance su ba.

Acewar Obi Najeriya ta samu ci gaba mai yawa a zamanin mulkin Babangida, musamman a bangaren kudi.
Bugu da kari Obi ya bayyana cewa ya ji dadin yadda gaskiya ta bayyana akan zaben shekarar 1993, wanda aka dunga yadashi a matsayin daya daga cikin zabukan Najeriya mafi gaskiya da adalci.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Obi bai samu damar shiga cikin harabar gurin taron ƙaddamar da littafin ba, tare da wasu mutane da dama, bisa kulle kofofin shiga da aka yi bayan zuwan shugaban Kasa Bola Tinubu gurin.