Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da shirin ta na aurar da zawarawa 300 a Jihar.

Kwamishinan yada labarai da al’adu na Jihar Alhaji Yakubu Ahmad BK ne ya tabbatar da hakan a jiya Alhamis, a yayin fara rabon kayayyaki ga wadanda za su ci gajiyar Shirin.
Kwamishinan ya ce za a gudanar da bikin ne a ranar 27 ga watan nan na Fabrairu da muke ciki, inda ya ce gwamnatin ta shirya shirin ne tare da hadin gwiwar gidauniyar NANAS.

Alhaji Yakubu ya ce za a gudanar gatan ne a fadar sarkin Gandu da ke Jihar, inda ya ce shirin na bana zai fi na shekarar da ta gabata tsari.

Acewarsa gwamnan Jihar Nasir Idris ya samar da shirin ne domin tallafawa mata da maza da ke fadin Jihar.